Kamfanin dillancin labaran - ABNA - ya habarta cewa, malaman addini da masu ra’ayin rikau sun halarci wani taro kan “Hadin kai da kalubalantar kalaman kyama ga ‘yan gudun hijira da bakin haure” a Lisbon, babban birnin kasar Portugal. Cibiyar tattaunawa ta kasa da kasa ce ta shirya taron tare da halartar shugabannin addinai na Turai don zaman lafiyar Turai tare da goyon bayan ofishin kula da dimokaradiyya da kare hakkin bil adama na kungiyar tsaro da hadin gwiwa a Turai. Taron dai ya samu halartar ministocin kasashen Turai da ‘yan siyasa da masu tsara manufofi da masu ba da shawara na musamman da jami’an diflomasiyya da wakilai da kuma malaman addini da suka hada da malamin Shi’a Hujjatul-Islam Wal Muslimeen “Sayyid Ali Abbas Razawi” .

2 Nuwamba 2021 - 14:46